Laraba 1 Nuwamba 2023 - 09:00
13 ga Aban: Damar Tunawa da Yaƙi da Ƙasashen Mamaya da Ƙarfafa Taken “Mutuwa ga Amurka”

Hauza/ Majalisar Daidaita Ayyukan Cibiyoyin Ilimi na Hauza ta yi kira ga dukkan malamai, ɗaliban Hauza da sauran al'ummar juyin juya halin Musulunci da ke birnin Qum, da su halarci babban taron tunawa da ranar 13 ga Aban, wanda za a gudanar a haramin Sayyida Ma’asuma (S.A), domin sake nuna adawa da zalunci da manufofin Amurka da Isra’ila.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya labarta cewa, Majalisar Daidaita Ayyukan Cibiyoyin Ilimi na Hauza ta fitar da wata sanarwa dangane da ranar yaƙi da danniya da zaluncin manyan ƙasashe, wadda Ayatullah Alireza A’arafi, shugaban majalisar, ya sanya wa hannu.

Ga fassarar cikakkiyar sanarwar:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

Allah Ya yi alƙawarin taimakon waɗanda suke taimakon addininsa. Lallai Allah Mai ƙarfi ne kuma Mabuwayi.

Imam Khumaini (R.A) ya ce: “Amurka da Isra’ila maƙiyan Musulunci ne tun daga tushe, domin suna kallon Musulunci, Alƙur’ani da Sunna a matsayin abin da ke hana su cimma manufofinsu na wawashe dukiyoyin al’umma. Iran kuwa, ta hanyar bin Alƙur’ani da Sunna ne ta tashi tsaye ta yi juyin juya hali, har ta samu nasara a kansu.”

Ranar 13 ga Aban, wadda ita ce ranar ƙasa ta yaƙi da danniya da zaluncin manyan ƙasashe, wata muhimmiyar dama ce ta tarihi wajen sake bayyana ra'ayin yaƙi da danniya da kuma rera taken “Mutuwa ga Amurka”.

Wannan rana tana tunawa da manyan al'amura uku da suka faru a tarihin Iran: a shekarar 1343 (Hijira Shamsiyya)(1964M), lokacin da aka kori Imam Khumaini zuwa ƙasar Turkiyya; a shekarar 1357(1978M), lokacin da aka yi mummunar kisan gilla ga ɗalibai; da kuma a shekarar 1358(1979), lokacin da aka mamaye ofishin leƙen asirin Amurka da ke Iran.

Saboda haka, wannan rana ta zama alamar ɗaukaka, tsayin daka, bijirewa maƙiya da yaƙi da danniya a wajen al'ummar Iran, tare da nuna gazawa da wulaƙancin maƙiyansu.

A yau, godiya ga Allah, al'ummomin da ake zalunta kuma suke ƙarƙashin danniyar manyan ƙasashe da Isra’ila, musamman al'ummar Falasɗinu, sun waye sakamakon koyi da juyin juya halin Musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sun fara wani babban yunƙuri domin kwato ikon tafiyar da al'amuransu da kuma kawo ƙarshen tsarin mamaya, tare da samar da sabon tsarin duniya.

Tsayin daka da jajircewar al'ummar Falasɗinu da mayaƙansu, tare da sadaukar da rayukansu, sun rubuta wani sabon babi mai daraja a tarihin Musulunci da na wannan zamani. Haka kuma, sun sake nuna wa duniya ɗaukakar Musulunci da Musulmi, wadda ta ginu bisa imani da Allah Maɗaukaki.

Kamar yadda Allah Maɗaukaki Ya bayyana a cikin Alƙur’ani Mai Girma cewa:

“Kar ku raunana, kuma kada ku yi baƙin ciki, domin ku ne mafifita idan kun kasance muminai.” (Suratu Ali Imran: 139).

Makarantun Hauza kuwa, yayin da suke tunawa da Imam Khumaini (R.A), da irin bajintar da shahidai da sauran al'ummar Iran masu hangen nesa suka nuna wajen fafatawa da Amurka da sauran manyan ƙasashe masu danniya, sun jaddada muhimmancin tsayin daka da al'ummomin Musulmi suke yi wajen fuskantar Amurka da Isra’ila.

Haka kuma, suna jaddada wajibcin ci gaba da riƙe manufofin juyin juya halin Musulunci, tare da bin jagoranci da shawarwarin Imam Khamene'i (H).

Majalisar ta kuma yi kira ga ɗaukacin al'ummar Iran, musamman ɗaliban Hauza, ɗaliban jami'o'i da ɗaliban makarantu, da su sake fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin halartar bukukuwan tunawa da ranar 13 ga Aban. Hakan zai zama wata hanya ta yin Allah wadai da laifuffukan Amurka, Isra’ila da sauran masu danniya, da kuma karya gwiwar maƙiyan Musulunci tare da ƙarfafa gwiwar al'ummomin da ake zalunta, musamman al'ummar Falasɗinu.

Haka kuma, majalisar tana kira ga dukkan malamai, ɗaliban Hauza da sauran al'ummar juyin juya halin Musulunci da ke birnin Qum, da su halarci babban taron tunawa da ranar 13 ga Aban, wanda za a gudanar a haramin Sayyida Ma’asuma (S.A), domin sake nuna tsayin dakarsu da kuma yin Allah wadai da manufofin danniya na manyan ƙasashe da Isra’ila.

Ayatullah Alireza A’arafi Shugaban Majalisar Daidaita Ayyukan Cibiyoyin Ilimi na Hauza.

10 ga Aban, 1402 (01 ga Nuwamba, 2023).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha